18 Mayu 2026 - 13:50
Source: ABNA24
Iran: Jami'an Tsaro Sun Kai Hari Kan Sojojin Hayar Amurka Da Isra'ila

Ƙungiyoyin 'yan ta'adda da ke wakiltar Amurka da Sahayoniya sun shiga tarkon jami'an tsaron Iran a gundumar Bane na lardin Kurdistan

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cewar sashen hulɗa da jama'a na sansanin Hamza Sayyidush Shuhada (AS) na sojojin ƙasa na Rundunar Irgc ta hanyar ayyukan leƙen asiri na jami'an sirrin Imam Zaman AS na sansanin Hamza Sayyidush-Shuhada (AS), sun kama ƙungiyoyin 'yan ta'adda masu adawa da juyin juya halin Musulunci da ke zaune a arewacin Iraki, waɗanda Amurka da Isra'ila ke jagoranta, yayin da suke shirin jigilar manyan makamai da alburusai na Amurka zuwa cikin ƙasar, a gundumar Bane na lardin Kurdistan. 

An gano tare da kama manyan makamai da alburusan waɗannan miyagun mutane kuma ana ci gaba da ayyukan leƙen asiri don gano da kama dukkan masu hannu wajen cin amana a cikin ƙasar.

Sansanin Hamza Sayyidush Shuhada (AS) yana yi wa dukkan maau cin amanar ƙasa da kuma jagororinsu gargadi cewa, za a tunkari duk wani mataki na tsaro da ƙarfi, kuma suna shirye don mayar da martani mai cike da nadama ga masu aikata laifukan.

.........................

Your Comment

You are replying to: .
captcha